Mutane 7 sun suma a wurin taron yakin neman zaben Atiku a Kano


Aƙalla magoya bayan jam’iyar PDP su bakwai ne suka suma a wurin taron yakin neman zabenAtiku Abaubakar da ya gudana ranar Lahadi ciki har da mace guda daya.

Taron gangamin ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha dake birnin.

Jami’an tsaro ne suka samu nasarar ceto mutanen kana daga bisani aka samu aka farfaɗo da su.

Taron na yau dai ya yi armashi ga magoya bayan jam’iyar ganin yadda filin wasa ya yi cikar kwari dama wasu sassa na birnin.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like