Mutane 7 Sun Jikkata  A Wani Fada Tsakanin Sojoji Da Yayan Kungiyar IPOB  A Abia


A kalla mutane 7 suka jikkata a wani fada tsakanin sojoji da yayan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra. 

Akwai dai rahotannin dake cewa sojojin Najeriya da suka fito daga Birged ta 14 sun mamaye gidan Nmandi Kanu, inda suka bude huta kan yayan kungiyar ta IPOB. 

Amma kuma sojojin sun karyata wannan rahoton inda suka ce yayan kungiyar ta IPOB ne suka takalesu.

A wata sanarwa Oyegoke Gbadamosi, mataimakin daraktan hulda da yan jarida yace yayan kungiyar ta IPOB ne suka tsare hanyar da sojoji suke wucewa.

” Taron yayan kungiyar yan ta’addar IPOB ne tarewa sojojin bataliya ta 145 hanya lokacin da suke gudanar da zagayen nuna karfi a Umuahia babban birnin jihar Abia, ” sanarwar tace. 

” Sun dage kan cewa sojojin baza su wuce ba inda suka fara jifan sojojin da duwatsu da kuma fasassun kwalabe har takai da sun raunata wata mace dake wucewa ta gefen titi da kuma wani  soja mai suna Kolawole Mathew.”

Hakan yasa sojojin sun yi harbin iska domin watsa  masu fafutukar kafa kasar ta Biafra.

” Saboda haka ana shawartar jama’a da suyi watsi da jita-jita da kuma wasu hotunan karya  da ake yadawa na wadanda suka jikkata a rikicin. Tuni aka dauke sojin da kuma matar da ta jikkata zuwa dakin bada magani,” sanarwar tace. 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like