Mutane 5 aka kashe, 45 suka jikkata a harin kunar bakin wake a Maiduguri


Mutane biyu ne suka mutu yayin da wasu 45 suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai Garejin Muna dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Jaridar The Cable ta gano cewa lamarin yafaru ne ranar Asabar.

Usman Kachalla, daraktan dake kula da sashen ayyukan ceto a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ya ce yan kunar bakin wake biyu ne suka kai hari da misalin karfe takwas na daren ranar Asabar.

“An dauke waɗanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar domin samun kulawar likita,” Kachalla ya ce.

Ya kara da cewa mutane biyun da suka mutu sun mutu ne lokacin da suke samun kulawar likita a asibitin.

Koda a shekarar da ta gabata mutane da dama ne suka mutu a yankin na Garejin Muna.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like