Mutane 46 sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane a Nasarawa


Mutane 46 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hakumar Nasarawa ta jihar Nasarawa sun samu kubuta bayan da suka shafe kwanaki hudu a tsare.

Sulaiman Ibrahim Eya, daya daga cikin mutanen da ya yi magana da jaridar Daily Trust ya ce ” Muna cikin tafiya mun doshi Nasarawa lokacin da muka ga wasu motoci a gabanmu sai muka ji harbin bindiga sau uku hakan ya sa muka tsaya. Yan bindiga goma rike da AK-47 uku daga cikinsu sanye da kayan sojoji sun dauki mutane 48 daga cikin mu daga baya suka harbe biyu daga cikin mu wadanda yan Fulani ne kamar su.”

A cewarsa sun yi tafiya a kasa ta tsawon sa’o’i uku kafin a kyale su, su huta a kusa da wani dutse kana suka cigaba da tafiya washe gari kafin masu garkuwar su kira waya su bukaci kudin fansa.

Ya ce sai da babansa ya sayar da gonarsa kana yan uwa suka bayar da gudunmawarsu aka hada naira miliyan daya kafin a sako shi.

Haka batun yake ma ga sauran mutanen inda suka biya kudi daga dubu dari biyar zuwa miliyan daya yayin da waɗanda suka gaza bayar da nambar wayar yan uwansu aka lakada musu dukan kawo wuka.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like