Mutane 3 sun warke daga cutar Korona a jihar Imo


Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce an sallami masu dauke da cutar Coronavirus su uku daga cibiyar killace masu dauke da cutar ta jihar.

Da yake karin haske ranar Asabar kan matsayin masu cutar a jihar gwamnan ya ce an gwada mutanen basa dauke da cutar kamar yadda ka’idar hukumar NCDC ta tanada.

Ya ce cikin mutane 7 da suka kamu da cutar a jihar hudu ne ka dai suke da ita a yanzu.

Gwamnan ya ce za a cigaba da kula da sauran ragowar marasa lafiyar har ya zuwa lokacin da za su warke.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like