Mutane 257 ya yin da wani jirgin saman soja ya yi hatsari a kasar Aljeriya


Akalla mutane 257 suka mutu bayan wani jirgin saman soja ya fadi kusa da sansanin sojan sama na Boufarik dake wajen Algiers, babban birnin kasar.

Gidan Talabijin din Ennahar na gwamnatin kasar, ya ce jirgin na dauke da yawancin sojoji da kuma iyalansu ya fado kasa jim kaɗan bayan ya ta shi da safiyar ranar Alhamis.

An ce jirgin na kan hanyarsa ta zuwa garin Tindouf dake kudancin kasar lokacin da hatsarin ya faru.

A wata sanarwa an jiwo mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar na cewa mutanen da suka mutu sun hada da ma’aikatan jirgin goma da kuma fasinjoji 247 wadanda yawancinsu sojoji ne da kuma iyalansu.

Sanarwar ta kara da cewa ya zuwa yanzu ba iya tantance musabbabin hatsarin ba amma ana cigaba da bincike.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like