Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad

Babban sakatare a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Bauchi, Alhaji Shehu Ningi ya ce kusan mutane 15 suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya faru a kauyen Gwaskaram dake jihar.

Ningi ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Alhamis a Bauchi.

A cewarsa kwale-kwalen na dauke da fasinjoji da suka fito daga kauyen Gwaskaram akan hanyarsu ta zuwa kasuwar kauyen Yola Doka.

Ya ce lamarin ya faru ne a Kogin Gwaskaran dake karamar hukumar Bauchi a karshen makom da ya wuce.