Mutane 14 aka kashe a musayar wuta tsakanin barayi da yan bijilante a Katsina


Akalla mutane 14 aka kashe a musayar wuta tsakanin wasu da ake zargin barayi ne da kuma yan sakai a ƙauyen Tsamiyar Jino dake karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Lamarin ya haifar da fargaba da kuma zaman dar-dar inda mutane suka shiga neman mafaka.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Gambo Isah ya dora alhakin faruwar lamarin kan yan banga wadanda suka gaza daukar shawarar da rundunar yansandan jihar ta basu.

Isah ya ce yan sakan ne suka kaddamar da farmaki a mafakar barayin.

Ya ce barayi bakwai aka kashe yayin da bangaren barayin aka kashe mutum 7.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like