Mutane 130 aka kashe a rikicin Kajuru


Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya ce mutane 130 aka kashe a harin da aka kai wasu rugagen fulani a Kajuru ba mutane 66 ba kamar yadda aka fada tunda farko.

Da yakewa manema labarai dake fadar shugaban kasa jawabi bayan taron majalisar tsaron kasa da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja.

Gwamnan ya ce nan gaba kadan za a fitar da sunaye da kuma hotunan mutanen da suka mutu a rikicin..

Taron wanda aka dauki tsawon sa’a guda ana yi ya samu halartar gwamnan jihar Adamawa, Jibrila Bindow, Kashim Shettima na jihar Borno da kuma mambobin majalisar tsaron kasa.

El-Rufai ya bayyana cewa anyi kashe-kashen ne da gan-gan domin karar da wata al’umma.

A makon da ya wuce ne wasu maharan da ba a san ko suwaye ba suka kai farmaki rigar Fulani da dama dake yanki na Kajuru a karamar hukumar Jema’a dake jihar ta Kaduna.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like