Musha Dariya


SANTIN SABUWAR AMARYA… 
Wani mutum ne yayi sabuwar amarya.

Bayan kwana biyu sai abokan shi suka tambaye shi “Bala ya amarya?” Sai yace; Kai ni ana cewa mata tara suke basu cika goma ba, kai ni matata goma take cif don matata, Muslimatin, Muminatin, Kanitatin, Sadikatin, Sa’imatin,.. 

Kai har zuwa karshe sai suka ce kai amma kayi sa’a Allah ya bada zaman lafiya. Bayan watanni kadan sai suka hadu da abokansa sai suka ce Bala ya Musulimatin? Sai yace; “Ai yanzu ta zama  Muguwatin, Munafukatin, Kazamiyatin, Makiratin, Shegiyatin, Azzalumatin, kuma saura kiris ta zama Bazawaratin”


Like it? Share with your friends!

-5
205 shares, -5 points

Comments 12

Your email address will not be published.

  1. Har ayanzu aikin laifi ko izgili da Addini bai barmu ba wanda Gaskiya wannan irinsa ba dai-dai ba ne.
    Abun mamakine kun kaasa tan-tance wane abune na wasa har ayi dariyarsa!,Don Allah ku gyara babu kyau wasa da Addini.

You may also like