Mun shirya samar da Ruga a jihar Bauchi -Bala Muhammad


Gwamna jihar Bauchi,Bala Muhammad ya ce jiharsa a shirye take ta rungumi shirin gwamnatin tarayya na samar da Rugar fulani makiyaya.

Ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da yake magana da yan jaridar dake fadar shugaban kasa.

Gwamnatin tarayya ta samar da shirin kafa Ruga a matsayin wata hanya da za ta kawo karshen rikicin dake faruwa a tsakanin Fulani da Manoma amma wasu yankuna na kasarnan musamman jihohi dake kudu sun yi watsi da shirin.

A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya ce gwamnonin yankin kudu maso gabas dana kudu maso kudu basu bayar da fili ba a yankunan biyu domin tsugunar da Fulani makiyaya.

Amma da aka tambaye shi ko jihar Bauchi za ta rungumi shirin samar da ruga Muhammad ya ce:” Eh mai zai hana saboda yawan Fulani dake Bauchi ya kai kaso 60 zuwa 70 na mutanen jihar. Saboda haka dole muyi amfani da wannan damarmaki.”

Sanarwar tasa na nufin jihar ta shiga jerin sauran jihohi da suka rungumi shirin.


Like it? Share with your friends!

-1
70 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like