Mun kirkiru sabbin masarautu domin ragewa Sarki Sunusi nauyi


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kirkiri sabbin masarautu a jihar ne domin ragewa sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, nauyi.

Ya ce kalubalen masarautar Kano suna da girma da kuma yawan gaske saboda haka samar da wasu zai kawo cigaba kusa da jama’a.

Ganduje ya rattaba hannu kan dokar da ta kirkiri karin masarautu hudu a jihar inda aka barwa sarki Sunusi ikon mukin kanana hukumomi 10 a maimakon 44 da yake mulka a baya.

Sabbin sarakunan sun hada da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero, Ibrahim Abubakar II,Sarkin Karaye,Tafida Abubakar Ila sarkin Rano da kuma Ibrahim Abdulkadir Sarkin Gaya.

Mutane da dama na kallon sabon yunkurin kafa masarautun a matsayin wani salon yakar mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II wanda gwamnatin jihar ke zarginsa da taimakon abokan hamayyarta a zaben da ya gudana.

Da yake magana a wurin bikin da sarakunan suka shirya domin nuna godiyarsu bisa nadin da aka yi musu, Ganduje ya ce anyi dukkan abinda ya kamata na fannin shari’a akan sabuwar dokar saboda haka babu mahalukin da zai soketa.


Like it? Share with your friends!

1
79 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like