Mun Kai Alhazai Dubu 25 Saudiyya Cikin Dubu 43Wadannan alhazan sun hada da na jihohi dubu 33 da na jirgin yawo dubu 9 da ‘yan kai.

NAHCON da ke amfani da kamfanonin jirage 3 biyu na gida daya na Saudiyya na nuna kwarin guiwar kammala jigilar gabanin rufewar karshe ranar laraba.

Tun a lahadin nan a ka rufe damar shigar jiragen alhazai Saudiyya in ka debe FLYNAS na Saudiyya da kuma kamfanin MAX da ya damu izinin cigaba da jigilar.

Jagoran kamfanin FLYNAS a Najeriya Umar Kaila ya ce za su yi duk abu mai yiwuwa wajen tabbatar dukkan alhazai sun samu sauke faralin a bana bayan dakatar da damar tsawon shekaru biyu a sanadiyyar cutar annoba.

Umar Kaila

Umar Kaila

Kaila ya nuna takaicin yanda jinkirin da a ka samu daga jigilar alhazan Abuja ya jawo tsaiko da kuma asarar kimanin dala miliyan daya ga kamfanin.

Jami’ar labarun alhazan Fatima Sanda Usara ta ce akwai tsarin da a ka yi bana don walwalar alhazan da kuma cigaba da samar da abinci irin na Najeriya.

A gaskiya bana da yawa masu niyyar zuwa hajjin sun kwance damara don rashin samun VISA da kuma karancin kujerun da a ka samu da su ka gaza bukatun jama’a.

Akwai mamaki yanda mutane su ka nace da zuwa hajjin bana duk da tsadar da kujerar ta yi mafi tsanani a tarihi da hakan ke nuna marmarin musulmi kan wannan babbar ibada.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg