Mun Gode Da Dawo Da Kudaden Da Aka Sace – Buhari Ga Gwamnatin Swizilan


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Talata ya ce Najeriya na godiya marar adadi ga gwamnati da ‘yan kasar Swizilan gudumawarta a fagen dawo da martabar tattalin arzikin Najeriya ta hanyar dawo da kudaden da ‘yan Najeriya suka sace tare da jigesu a kasar.

A yayin da yake karbar takardar amincewa daga jakadar kasar Swizilan, Mista George Steiner, a fadar gwamnati da ke Abuja, shugaba Buhari ya ce dawo da kudaden da aka sace tare da shiga cakanin matsalar ta’addanci a Arewa maso Gabas da gwamnatin kasar Swiz ta yi ya nuna kasar na kaunar ci gaban Najeriya.

“muna godiya ga kasar Swizilan bisa yarda da ta yi na dawo da kudaden Najeriya da aka sace aka boye a kasar”. Inji Buhari.

Buhari ya kara da cewa, irin rawar gani da gwamnatin kasar ke takawa a Arewa maso Gabas musamman a bangaren taimakon ‘yan gudun hijira, abin jinjina ne. Daga karshe ya tabbatarwa jakadar kasar Swizilan da cewa, kyakyawar alakar kasar da Najeriya za ta ci gaba da karfafa.

Shi ma a nashi bangare, jakadan kasar ya ce gwamnatinsu za ta ci gaba da taimakon Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya a kasar, musamman a arewa maso gabas.

“mu na da alaka mai karfi da Najeriya. Jin dadinmu ne mu taimaka a wasu al’amuran Najeriya” inji jakadan.

Ambasada Steiner ya gaya wa Muhammadu Buhari cewa gwamnatin Swizilan za ta kulla kyakyawar alaka mai karfi a bangaren tattalin arziki da Najeriya wanda zai sa ta amfana, inda ya bayyana cewa hakan na nuni da alamun kasar za ta turo da manyan masu zuba hanun jari.

Har Ila yau, shugaba Buhari ya karbi takardar amincewar fadada tafkin chadi daga jakadan kasar Belgium, tare da sabon jakadan kasar Hungary a Najeriya.


Like it? Share with your friends!

-3
93 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like