Mun Amince Mu Hada Kai Domin Ci Gaban Jihar Kano, Cewar Gwamnan Ganduje Da Sarkin Kano Baya Sun Sasanta Rikicinsu


Shugaban Gwamnonin Nijeriya, Kayode Fayemi da wasu masu fada a ji a kasar nan sun yi nasarar kawo karshen sabanin dake tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, kamar yadda majiyar ta Daily Nigerian ta rawaito.

Majiyar ta kara da cewa an kwashi tsawon lokaci ana tattaunawa tare da yi wa mutane biyun nasiha da shawarwari kafin daga bisani aka sasanta su.

Shugaban Gwamnonin zai yi wa shugaba Buhari bayani kan ganawar sulhun da aka yi a daren jiya Juma’a a Abuja.


Like it? Share with your friends!

-2
133 shares, -2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like