Mummunan Hadarin Mota Ya Ci Rayuka 18 A Jihar Gombe


INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN

A jiya Laraba (10-10-2018) Allah Madaukakin Sarki ya karbi rayukan mutane 18 sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da su akan hanyarsu na zuwa kasuwa.


Mamatan sun fito ne daga garin Jimin dake karamar hukumar Darazo a jihar ta Bauchi, inda za su tafi cin kasuwa a karamar hukumar Dukku jihar Gombe hatsarin ya rutsa da su, dukkan mamatan ‘yan gari daya ne, kuma dukkanninsu ma’aurata ne masu tarin iyalai.

Muna kira ga gwamnatin Baba Buhari Mai gaskiya da ta kawo tallafi ga iyalan wadannan mamata.

Sun mutu akan hanyarsu na tafiya neman halal, Allah Ka yafe musu
Allah Ka jikansu.

Allah Ka sa sun dace da mutuwar shahada.


Like it? Share with your friends!

1
72 shares, 1 point

Comments 7

Your email address will not be published.

  1. Inna lil lahi was INA ilaihi raaji un Allah gasu gareka,sun fita neman abinci ya Allah, Ya Allah KA Rahamcesu

You may also like