Mulkin Buhari Annoba Ne – Shugaban Talakawa


An bayyana mulkin Shugaban kasa Buhari a matsayin wats fitina da Annoba ga jama’ar Najeriya musamman al’ummar yankin Arewa, wadanda sune suka zabe shi amma sun fi sauran jama’ar kasar dandana azaba mai dadi a mulkin na shi.

Shugaban rundunar Talakawan Najeriya Alhaji Imrana Nas ya tabbatar da haka a yayin wani taron manema labarai da yayi a Kaduna.

Shugaban talakawan ya cigaba da cewar ya zama wajibi a gareshi ya fito yayi Allah wadai da shugabancin Buhari, sakamakon abin da ya kira cin amanar ‘yan Arewa da Buhari yayi a zangon mulkin shi na farko, inda ya tattara duk wani aiki da cigaban kasa ya jibge a yankin Kudancin Najeriya, ya bar ‘yan uwanshi ‘yan Arewa cikin bakin talauci da zubar da jini ba tare da ya damu ba.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Karba yake yi. Mulkin Buhari alkhairi ne gam yan Nigeria badon Aamin zaman lafiya ba ina ya isa ya yi zama da manema labaru. Wanda kaji tana sukan mulkin duk to imma azzalumi ne yanzu an hana shi zaluncin, ko an biyar shi ne don yaci mutuncin Shugaba.

You may also like