Muhimmiyar sanarwa DAga Gwamna Ganduje


Mai Girma Gwamnan Jihar Kano , Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na kira Ga daukacin al’ummar Jihar Kano da a kwantar da hankula, a zauna lafiya tare da girmamawa da ganin mutuncin juna musamman a wannan lokaci da mu ke ciki.

Mu sani cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma shine tushen kyautatuwar rayuwa da ci gaba a kowanne lokaci.

Jihar Kano ta mu ce baki daya. Don haka mu guji aikata duk wani abu ko kalamai da ka iya haifar da rashin zaman lafiya sakamakon sabanin ra’ayin siyasa ko makamancinsa.

Mai Girma Gwamna na kira ga iyaye da shugabannin al’umma su sa ido kan ‘ya’yansu da jama’arsu, su kuma tsawatar yayin da aka ga suna kokarin aikata ba daidai ba ko kuma daukan doka a hannunsu.

Hukumomin tsaro za su ci gaba ta ayyukansu na tabbatar da zaman lafiya da kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma a ko’ina a fadin Jihar Kano.

Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Allah ya taimaki Jihar Kano da daukacin al’ummar Jihar Kano. Amin.

Sako daga:
MALAM MUHAMMAD GARBA
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano
11/3/2019


Like it? Share with your friends!

1
61 shares, 1 point

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like