Motoci sun fada cikin kogi a Anambra


Motoci hudu ne a ranar Laraba suka fada cikin kogin Nnobi dake jihar Anambra bayan wasu jerin hatsura.

Hatsarin ya faru ne akan titin Ideani-Nnobi dake karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra.

Motocin da hatsarin ya rutsa da su sun hada da wata tankar mai, babbar mota kirar Marsandi, motar bas L300 da kuma J5.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Haruna Muhammad ya ce kwamishinan yan sandan jihar, John B Abang ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru.

Ya ce tawagar yan sanda dake sintiri karkashin jagorancin DPO na caji ofis din Nnobi sun gaggauta isa wurin inda suka samu nasarar ceto mutanen da abin ya rutsa da su kana suka garzaya da su asibitin Moon & Fatima dake Nnobi.


Like it? Share with your friends!

1
52 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like