Motar tirela ta kashe masu talla a gefen titi 10 a jihar Kebbi


Wata motar tirela ta kwace a garin Jega dake jihar Kebbi inda ta kashe mutane 10 masu kasa kaya a gefen titi.

Wani da ya ganewa idonsa abin da yafaru ya bayyana cewa motar na tahowa ne daga bangaren Koko/Yauri lokacin da lamarin ya faru.

Sauran mutane 46 da suka jikkata a lamarin na can suna samun kulawa a asibitin garin Jega.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa yawancin wadanda lamarin ya rutsa da su masu sayar da kayayyaki ne kamar su,Lemo, Biredi,Ayaba da sauransu.

Ya ce “Hatsarin yafaru da safiyar yau. Ina tunanin motar ta taho ne daga Lagos ko kuma Ibadan a yankin kudu maso yamma.Ta kwace a hannun direban lokacin da take shiga Jega ta bangaren Yauri/koko inda ta yi kan masu talla a gefen titi.”


Like it? Share with your friends!

-1
81 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like