Motar jami’an FRSC ta yi hatsari lokacin da suke bin wani direba


Wata mota kirar Hilux mallakin hukumar kiyaye hadura ta kasa,FRSC ta yi hatsari lokacin da suke biyo wani direba da ake zarginsa da saba ka’idojin hanya a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Motar tayi taho mu gama da wata mota kirar Toyota dai-dai lokacin da suke bin direban.

Lamarin yafaru ne akan hanyar Oyo- Ibadan.

Mai magana da yawun hukumar ta FRSC a jihar,Oluwaseun Onijala ya tabbatar da faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

2
89 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like