Ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofer da ke kaddamar da sabon rahoton a gaban manema labarai a wannan Talata, ya zargi jam’iyyar masu tsananin kyamar baki da aikata fiye da rabin ta’adin miyagun aiyukan, baya ga wadanda aka gudanar a yayin gangamin adawa da matakan yaki da corona a wasu sassan kasar.

Wannan ne dai alkaluma mafi muni da hukumomin kasar suka bijiro da su na masu aikata barna, idan aka yi la’akari da rahotannin da suka fitar a shekarun da suka wuce, lamarin da ke zame wa kasar wata babbar barazana.