Ministan tattalin arzikin Ajantina ya yi murabus | Labarai | DWMinistan Tattalin Arzikin kasar Ajantina Martin Guzman ya yi murabus daga mukaminsa, sai dai har yanzu tsohon ministan da ya fara aiki tun 2019 bai bayyana dalilansa na daukar wannan mataki ba. Amma a wasikar barin aikin da ya aikewa shugaban kasa Alberto Fernandez, ya shawarci gwamnati ta dinke barakar cikin gida don kar wanda zai gaje shi ya sha irin wahalar da ya sha.

A matsayinsa na ministan tattalin arziki, Guzman ya jagoranci sake tattaunawa kan bashin dala biliyan 44 (€42.19) da asusun lamuni na duniya IMF, wanda Argentina ta dage cewa ba za ta iya biya ba.

Murabus din Guzman ya zo ne a dai-dai loakcin da Ajantina wacce ke zama kasa ta biyu wajen fitar da masara a duniya, kuma ta daya a fitar da waken soya da abinci da aka sarrafa amma ta fada matsalar tattalin arziki da ya shafi faduwar darajar kudin kasar da kuma hauhawar farashin kaya da karancin man diszel da taki.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg