Ministan man fetur ya bayyana dalilin wahalar man fetur a wasu jihohi


Karamin ministan albarkatun man fetur, Dakta Ibe Kachikwu, ya ce an samu dogayen layuka a gidajen man fetur da ke wasu jihohin kasar nan ne sakamakon gibin da aka samu a jigilar mai, ya ce dogayen layukan ba su da alaka da karancin man fetur.

Da ya ke magana da ‘yan jarida a Legas, Kachikwu ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar cewar za a yi karin farashin man fetur.

Ministan ya yi wannan jawabi ne ga manema labaran a wurin bude wani taro na kasa da kasa a kan man fetur da iskar gas, wanda aka yi a Legas.
Dakta Ibe Kachikwu, ministan man fetur

Ya ce babu wani lokaci da jagororin gwamnati suka zauna, suka yi magana a kan karin farashin man fetur da jama’a ke cigaba da yada wa.

“Na samu damar kewaya wa wasu gidajen man fetur kuma na gani da idona yadda dogayen layika suka ragu a gidajen man. Batun karin farashin man fetur wata magana ce da ke bukatar duba na tsanaki.

“Gwamnati za ta mu’amalanci ‘yan kasuwar man fetur kafin ta zartar da kowanne hukunci.

“Akwai damuwa a kan yadda dogayen layi suka dawo gidajen man fetur duk da irin tabbacin da NNPC ta bayar,” a cewar Kachikwu.

Ya bayyana kwarin gwuiwarsa a kan NNPC da jagororinta, ya na mai bayyana cewar tuni aka warware matsalar da aka samu wajen jigilar man fetur da ta haddasa dawowar dogayen layuka a gidajen mai.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like