Miliyan ₦500 Buhari ya rabawa mutanen Adamawa


Shugaban kasa,Muhammad Buhari raba kudi har naira miliyan 500 ga mabukata dake jihar Adamawa.

Buhari ya raba kudin ne daga watan Agustan shekarar 2017 zuwa watan Agustan shekarar 2018 karkashin shirin daukaka darajar gidaje wanda bangare ne na shirin bawa iyalai masu karamin karfi kudade bisa wasu sharuda.

Mr Zeghun Joseph, jami’in tsare-tsare na shirin shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litinin a Yola.

Joseph, ya ce shirin wani bangare ne na cika alkawarin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya dauka a lokacin yakin neman zabe kuma an tsara shi ne domin a tallafawa mutane masu karamin karfi.

“Ya zuwa yanzu shirin gwaji da aka fara a Adamawa cikin watan Agustan shekarar 2017 da mutane 8653 suka amfana a kananan hukumomi shida.

“Duk wani gida da aka zaba ya karbi kyautar ₦5000 a kowane wata,” Joseph ya ce.

Bayan samun nasarar shirin na gwaji shugaban kasar ya bayar da umarnin kara saka wasu iyalan dake da bukata

Ya zuwa yanzu dai mutanen dake amfana da shirin ya kai 13,520.


Like it? Share with your friends!

-2
92 shares, -2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like