Merkel ta yaba dangantakar kasa da kasa | Labarai | DWMerkel wadda ta baiyana haka a birnin Berlin a taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta baiyana farin ciki da cewa shugaban Amirka ya sake samar da wani yanayin kawance da kowace kasa za ta yi abin da ya kamata.

Ta kara da cewa ya kamata kungiyar tarayyar Turai ta cigaba da tattaunawa da Rasha duk da banbance-banbance da ke tsakaninsu kan batutuwa da suka shafi tsaro da rikicin kasashen Ukraine da Siriya.

Shugabar gwamnatin Angela Merkel ta kuma ce akwai bukatar kasashen na Turai su tsara tare da tuntubar juna kan manufofinsu na annobar corona da kuma sake bude iyakoki. 

Shi ma da yake tsokaci shugaban Faransa Emmanuel Macron yace ya kamata a yi taka-tsantsan kada a sake shigo da wasu sabbin nau’in kwayar cutar zuwa cikin kasashe.
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.