Melaye ya nemi kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun da ya kore shi daga majalisa


Dino Melaye sanata mai wakiltar mazabar arewacin Kogi a majalisar dattawa ya nemi kotun daukaka kara da ta jingine hukuncin kotun sauraron kararraki zabe ta jihar Kogi da ta kore shi a matsayin wakili a majalisar dattawa.

Ranar 23 ga watan Agusta ne kotun ta soke zaben da ya bawa Dino Melaye nasara kana ta umarci hukumar zabe ta INEC da ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90.

Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da dantakarar jam’iyar APC, Smart Adeyemi ya shigar gabanta.

Rashin gamsuwa da hukuncin kotun, Melaye ta hannun lauyansa, Ricky Tarfa ya shigar da kara a gaban kotun daukaka karar.

A takardun daukaka karar mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Satumba Melaye ya kalubanci hukuncin bisa dogaro da wasu hujjoji.

Babban hujjarsa ta neman a soke hukuncin ita ce sunan da mai kara shigar da kara da shi shine “Dino Melaye” wanda hakan ya saba da sunan, Melaye Daniel Dino da mai daukaka kara yayi amfani da shi a fom din da ya cike na hukumar zabe .

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like