Melaye Bai Dace   Ya Zama Sanata Ba -Gwamna Bello 


Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya shawarci majalisar dattawa da ta tabbatar majalisar na kunshe da mutane masu daraja da kuma mutunci domin kare mutuncin majalisar a idon jama’a .

Bello ya bayyana hakane lokacin da yake ganawa da manema labarai dake fadar shugaban bayan da ya ziyarci mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo. 

  Gwamnan yace Sanata Dino Melaye dake wakiltar mazabar Kogi Ta Kudu a majalisar bai dace da zama Sanata ba. 

Ya shawarci majalisar ta dattawa da su fitar da bata gari daga cikinsu kada jama’a suce dukansu ba mutanen kirki bane. 

Amma ya bayyana cewa babu wani rikici da yake faruwa a jiharsa, inda yace jihar kogi na cikin zaman lafiya. 

“Anata aiyuka, kowa yana cikin murna, ana biyan albashi akan lokaci, muna cigaba sosai, “yace. 

Kan zargin da Dino Melaye yayi cewa gwamnan ya ware kudi naira biliyan daya domin ayi masa kiranye Bello yace”wannan tunaninsa ne,mutanen mazabarsa ne suka yinkuro domin suyi maganinsa ta hanyar da tsarin mulki ya basu dama.” 

Yace yaje fadar shugaban kasa ne domin ya sanar da mukaddashin shugaban kasa irin cigaban da aka samu a jihar. 

Comments 0

Your email address will not be published.

Melaye Bai Dace   Ya Zama Sanata Ba -Gwamna Bello 

log in

reset password

Back to
log in