MDD: Yakin Ukraine ya mamaye muhawara | Labarai | DWA muhawarar da suka tafka a rana ta farko, shugabanin da za su kwashe tsawon mako guda suna tattaunawa sun nuna damuwa kan kalubalen da duniya ke fuskanta da suka hada da yunwa da matsalar sauyin yanayi da kuma irin illar da mamayar Rasha a Ukraine ta haifar na hauhauwar farashin kayayyaki da na abinci da ma makamashi.

Yayin da yake jawabi a zauren taron ta kafar bidiyo, shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya zargi Rasha da haifar da matsalar karancin cimaka da gangan. Ya kuma dora wa Moscow alhakin kawo cikas ga fitar da kayayyaki daga Ukraine da ke kan gaba wajen noma.

Shi ma da ya ke magana a kan batun cimaka, firanministan Spain Pedro Sanchez cewa ya yi, shugaba Vladmir Putin na yi wa kasashen duniya bita da kulli da batun abinci. Ya kuma kara da cewa babu zaman lafiya idan ana fama da yunwa, kazalika ba za a iya magance matsalar yunwa ba tare da zaman lafiya ba.

A nasa jawabin, firanministan Japan Fumio Kishida ya yi kira kan yi wa kwamittin sulhun Majalisar Dinkin Duniya garanbawul, ya bayyana rashin jin dadinsa kan gazawar da aka yi na mayar da martani ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine saboda kariyar da Rashar take da shi na kujerar dundundun a kwamitin sulhu. 
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg