MDD na son a yi binciken kashe-kashe a Sudan | Labarai | DWMajalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga hukumomin kasar Sudan da su kaddamar da bincike mai zaman kansa, bayan kisan da jami’an tsaron kasar suka aikata a kan masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin soja a kasar.

Cikin wata sanarwar da shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar, Michelle Bachelet ta fitar musamman kan kisan ‘yan Sudan din tara a jiya Alhamis, jami’ar ta nuna damuwa kan abin da ‘yan sanda suka yi duk da bayanan da suka yi na cewar ba za su amfani da harsasan gaske ba a kan fararen hula.

Mutum 113 ne dai jami’an suka mutu a Sudan, tun bayan karbe iko da sojoji suka yi a watan Oktobar bara, kuma ya zuwa yanzu babu wani da aka dora wa alhakin kisan fararen hulan.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg