Taron wanda za a gudanar a Geneva na zuwa ne bayan mika bukatar hakan daga bangaren wakilan kungiyoyin hadin kan musulmai na Pakistan da kuma Afghanistan, kawo yanzu kasashe 89 na duniya ne suka marawa batun baya.

Kiran taron na mussaman baya ga babban taron kungiyar dake gudana sau uku a shekara, na bukatar samun goyon bayan kasashe kaso daya bisa uku a kungiyar mai mambobi 47.

Kungiyar Taliban dai ta sami nasarar kwace ikon Afghanistan a ranar Lahadin bayan da shugaban kasar Ashraf Ghani ya fice daga kasar a yayin da kungiyar ta sami nasarar kutsawa babban birnin kasar Kabul.