Mazauna Kaduna sun kona wani mai garkuwa da mutane


Mazauna unguwar Kawo dake jihar Kaduna sun kashe wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne lokacin da suka yi kokarin sace wani.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa rikici ya fara ne da misalin karfe 8 na safe lokacin da mazauna yankin suka samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane su uku na kokarin sace mutane a yankin.

Mazauna yankin sun rufe duk wata hanyar shiga da fita unguwar inda suka rufarwa masu garkuwar har ta kai sun kama daya daga ciki.

Bayan da jami’an ƴansanda suka samun labarin cewa ana hargitsi a yankin sun gaggauta zuwa wurin domin tarwatsa mutanen har ta kai ga sun kashe mutum wanda aka ce mai sayar da lemo ne tare da jikkata wasu da dama.

Wani mazaunin yankin ya shedawa jaridar cewa jami’an ƴansanda sun samu nasarar kama mutum daya daga cikin masu garkuwar bayan da suka kwato shi daga hannun fusatattun mutanen unguwar.


Like it? Share with your friends!

-1
67 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like