Mazan Najeriya Sun Fi Na Afirka Ta Kudu – Inji ‘Yar Afirka Ta Kudu Da Dan Najeriya Ya Ba Ta Kyautar Mota


Wata mata ‘yar kasar South Africa ta bayyana cewa mazajen Nijeriya sun fi takwarorinsu na kasar South Africa, don haka take bai wa ‘yan uwanta matan South Africa shawarar su nema wa kansu mazajen Nijeriya.

Matar ta bayyana hakan a shafin sada zumunta na ‘Twitter’ bayan ta samu kyautar tsaleliyar mota daga mijinta ɗan Nijeriya. Take cewa duk da tsangwama da kyamar da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a hannun ‘yan South Africa, mazajen Nijeriyan dai sune zaɓin da ya fi alheri.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like