Mayakan Taliban sun kashe yan sandan Afghanistan 28


Kungiyar Taliban ta kaddamar da wasu jerin hare-hare kan shingen binciken jami’an tsaro inda ta kashe yan sandan Afghanistan 28 a cewar wani jami’in gwamnati.

Zelgai Ebadi, mai magana da yawun gwamnan Uruzgan ya ce yan kungiyar ta Taliban sun yi wa yan sandan jihar da kuma na gwamnatin kasa tayin su mika wuya kafin su barsu su tafi gidajensu idan suka mika wuya ranar Talata da daddare ” Amma bayan da suka kwace bindigoginsu sai yan Taliban suka kashe su baki ɗaya.”

Mai magana da yawun kungiyar,Qari Mohammad Yousuf Ahmadi ya ce sune suka kai harin inda ya ce an kashe yan sandan ne bayan da suka ki mika wuya.

Shima wani jami’in gwamnati da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da mutuwar yan sanda 28 inda ya kara da cewa uku sun samu nasarar tserewa.

Ebadi ya ce daga bisani jami’an tsaron , Afghanistan sun samu nasarar sake karbe iko da shingen binciken.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like