Mayakan da aka bawa horo a Libya ne suke taimakawa Boko Haram – Buhari


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce mayaka da aka bawa horo a Libya a tsawon shekaru 43 da marigayi,Muammar Gaddafi ya shafe yana mulki sune suke tayar da zaune tsaye a yankin Afrika ta Yamma.

Buhari ya fadi haka ne ranar Asabar a Abuja lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Kodebuwa,Alassane Quattara a wurin taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 56.

Taron ya gudana ne a dakin taro dake fadar shugaban kasa a Abuja

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya habarto Buhari na cewa tashin hankalin da aka samu a Libiya wata barazana ce ga yankin Sahel da kuma yankin kudu da hamadar Sahara.

A cewar Buhari an bar mayakan ba tare da wani abun yi ba da za su rayu “kawai sai harbi da kisa,” sune a yanzu suke rayuwa ta hanyar aikata laifuka da kuma ta’addanci.

Ya ce mayakan su suka hade da Boko Haram suke tayar da hankali a yankin arewacin Najeriya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 16

Your email address will not be published.

You may also like