Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji sama da 840 a Borno -Ndume


Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin sojoji ya ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 840 daga shekarar 2013 ya zuwa yanzu.

Ya ce an binne sojojin da suka mutu a makabartar sojoji dake Maiduguri.

Ndume ya ce adadin bai hada da sojojin da yan ta’addar suka kashe, amma aka binne su a wata makabartar sojoji ta daban.

Dan majalisar ya yiwa manema labarai jawabi bayan da kwamatinsa ya dawo daga ziyarar da suka kai Maiduguri.

Ya ce yayin ziyarar mambobin kwamitin sun gano cewa sojoji basu da isassun kayan yaki da za su fuskanci Boko Haram.

Ya kara da cewa yawan sojojin dake yaki da Boko Haram sun yi kadan inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara daukar mutane aikin soja.

Ya ce tuni kwamitin majalisar ya fara bincike kan zargin da ake wa wasu kungiyoyin sa kai na hada baki da yan Boko Haram.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like