Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 10 tare da kona gidaje sama da 100 a Borno


Akalla mutanen da basu gaza goma ne ba suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata lokacin da wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan kauyen Molai dake wajen birnin Maiduguri a jihar Borno a cewar mazauna yankin.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a yankin na Molai dake karamar hukumar Jere ta jihar.

Mayakan sun kuma samu nasarar kona gidaje sama da dari a ƙauyukan Molai da Maiboriti da kuma shingen binciken sojoji a cewar wata majiya da ta tatttauna da jaridar Daily Trust.

Wani mazaunin yankin, Mallam Isa Kagama ya ce sun rasa mutane bakwai a harin.

” Akalla mutane 10 aka kashe ciki har da sojoji. Farar hula uku a kauyen Maiboriti da kuma wasu hudu a Molai.

“Munga barnar da bamu taba ganin irinta ba a baya, sun lalata cibiyar samar da hasken wutar lantarki dake samar da wuta ga birnin Maiduguri baki daya kalli gidajen mu sun mayar da mu marasa gidaje,”Mallam Isa ya fada sa’ilin da yake sheka kuka.

Kauyen Molai dake da tazarar kilomita 4 daga birnin Maiduguri ya sha fuskantar hare-hare daga mayakan kungiyar ta Boko Haram a yan shekarun nan.

Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Sagir Musa ya tabbatar da faruwar harin sai dai ya ce dakarun sojoji sun samu nasarar dakile shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like