Mayakan Boko Haram sun kashe manoma biyu a Borno


Manoma biyu aka harbe har lahira a wani hari da ake zargin mayakan Boko Haram da kai wa a kauyen Kautikari dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Wata majiya da ta tabbatarwa jaridar The Cable faruwar lamarin ta bayyana cewa manoman suna daf da kammala aiki a gonakinsu lokacin da yan ta’addar suka kai harin inda suka kashe biyu daga ciki sauran kuma suka gudu cikin daji.

Majiyar ta bayyana cewa manoman basu yi tsammanin harin ba inda ya kara da cewa akwai sojoji a kauyen Kwada dake kusa da Kautikari.

Manoman da suka mutu a harin sun hada da Ali Yanga da Wahum Dura.

Kautikari kauye ne dake da tazarar kilomita daga garin Chibok inda mayakan na Boko Haram suka sace wasu yan matan makarantar sakandare a shekarar 2014.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like