Mayakan Boko Haram sun kai hari a Adamawa


Wasu mutane da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wani gari dake karamar hukumar Michika ta jihar Adamawa ranar Litinin.

Wata majiya ta fadawa jaridar The Cable cewa mayakan sun farma garin da daddare.Mazauna garin sun gudu cikin dazuka da kuma tsaunukan dake kusa domin gujewa fushin yan ta’addar.

Mayakan kungiyar tunda fari sun kai hari kauyen Shuwa dake karamar hukumar Madagali ta jihar da misalin karfe 6:45 na dare .

Da aka tuntubi,Othman Abubakar mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Adamawa, ya ce ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bashi da cikakken bayani akan harin da aka kai.

Jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Sani Usman Kukasheka amma abin yaci tura.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like