Mayakan BH sun kashe ma’aikatan agaji 5 da suka sace


Akalla ma’aikatan agaji su biyar da aka sace a jihar Borno mayakan Boko Haram suka hallaka su.

Ma’aikatan agajin na tafiya ne daga Maiduguri ya zuwa Monguno dake arewacin jihar ranar 29 ga watan Yuni lokacin da mayakan Boko Haram suka kai musu harin kwanton bauna.

A wani fefan bidiyo da kungiyar ta wallafa a shafukan Intanet wani daga cikin mayakan kungiyar da yayi magana da harshen Hausa ya ce an kashe mutanen ne saboda suna aiki da kafirai.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like