Mawaki Shariff Aminu Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Zai Iya Zuwa Har Kotun Koli – Gwamna Ganduje


Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa mawakin da aka yanke wa hukuncin kisa mai suna Yahaya Sharif-Aminu, wanda yai batanci ga Annabi yana da damar daukaka kara har zuwa kotun koli.

Gwamnan Ganduje ya fadi haka nr yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a Abuja bayan ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan baku manta ba dai wata Kotun Musulunci a Kano ce ta yanke wa Aminu Shariff hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga manzon Allah, a wata wakarsa da ta yi ta yawo a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

A cewar Gwamna matashin ya riga ya daukaka kara yace Kum Za’a cigaba da shari’a har kotun koli a halin yanzu muna jiran hukunci ne kawai – inji Gwamna Ganduje


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like