Matsalar tsaro na kara ta’azzara a gwamnatin Buhari – Jonathan


Tsohon shugaban kasa, Gudluck Ebele Jonathan ya ce matsalar tsaro na cigaba da ta’azzara karkashin mulkin Buhari.

Jonathan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar taaziya gidan Reuben Fasoranti shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere a gidansa dake Akure babban birnin jihar Edo.

Wasu yan bindiga ne da ba’asan ko suwaye ba suka harbe Funke Olakunrin yar gidan shugaban kungiyar ta Afenifere akan hanyar Benin zuwa Ore lokacin da take komawa jihar Lagos bayan ta kai wa mahaifinta ziyara a ranar Juma’a.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta kafa wani sashe na musamman da zai yi yaki da ayyukan masu garkuwa da mutane kuma barayi yan bindiga.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like