Hare-haren yan bindiga tare da garkuwa da mutane sun ta’azarra a wannan watan na Apirilu a kasar mai mafiya yawan al’umma a nahiyar Afirka. A makon da ya gabata kachal, akalla mutane sama 240 aka salwantar da rayuwarsu wasu gwammai kuma aka yi garkuwa dasu.

Yan adawa da ma daidaikun al’umar kasar sun zargi shugaban da gazawa wajen tabbatar da tsaro a yankunan kasar, inda aka kiyasta cewa kimanin mutane sama da miliyan biyu ne┬áke gudun hijira a kasashe makwabata bayan hallaka wasu sama dubu talatin da shida.