Matattu sama da miliyan daya ne za su kada kuri’a a cewar,Secondus


Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, ya ce kundin rijistar masu kada kuri’a na kunshe da sunan matattu sama da mutane miliyan ɗaya.

Secondus ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wani taron gaggawa da jam’iyar PDP ta gudanar a Abuja.

Ya ce jam’iyar PDP tana da shedar cewa ” matattu sama da 1,050,051 ne za su kada kuri’a a zaben da za ayi.”

A cewarsa,” rijistar masu kada kuri’a na dauke da bayanan wadanda suka mutu. An buga tare da raba katin zaben na din-din a fadin kasa baki dake dauke da bayanan wasu mutane da suka mutu.”

Secondus ya kuma zargi hukumar zabe ta INEC da kitsa shirin sauya alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa na ranar Asabar mai zuwa.


Like it? Share with your friends!

-1
94 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like