Matasan PDP Sun Farwa Magoya Bayan APC A Garin Nafada


Duk da yadda cewar kowa daga cikin ‘yan takarar kujerar Gwamna ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, za a yi siyasa ba tare da tashin hankali ba har Allah Ya zabi wanda yake so.


A jiya da dare wasu matasa dake ihun sai Bayero sun farawa tawagar yakin neman zaben Alh. Inuwa Yahaya da jifa daga cikin gida a cikin garin Nafada.

Wannan bashi ne fari da Matasan jam’iyar PDPn suka fara irin wannan ta’addancin ba domin sun yi irin sa a garin Deba, wanda suka fito da safe suka kona kayyakin jam’iyar APC kafin su shiga garin.

Wasu magoya bayan APC sun yi kira ga hukumomin tsaro a jihar Gombe da shiga cikin lamarin domin siyasa ba yaki bane na zubda jani.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like