Matar Yahaya Bello ta gamu da hatsarin mota a kusa da Kabba


Mako guda bayan da jirgi mai saukar ungulu na mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya fado lokacin da yake sauka a garin Kabba kwatsam sai gashi,Amina Yahaya Bello uwargidan gwamnan jihar ta gamu da iftila’in hatsarin mota a yankin.

Onoghu Muhammad, jami’in yada labaran gwamnan shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Muhammad ya ce hatsarin yafaru ne a wajejen Oshokoshoko dake kusa da Kabba lokacin da matar gwamnan da kuma wasu masu taimaka mata ke kan hanyarsu ta zuwa Isanlu domin halartar taron gangamin yakin neman zabe na mata.

Jami’in yada labarai ya bayyana cewa hatsarin ba mai muni bane.

A karshe ya bayyana cewa gwamnatin ta godewa Allah da ya tseratar da mutanen ba tare da samun raunuka ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like