Matar Messi ta haifi d’a namiji


Lionel Messi, ya sanar da haihuwar dansa na uku mai suna ‘Ciro’ Matar zakaran kwallon kafar ta haihu ranar Asabar.

Dan wasan ya bayyana dalilai na kashin kansa da suka sanya shi ficewa daga tawagar yan kwallon kafar kungiyar da yake bugawa wasa ta Barcelona da suka buga wasa da kungiyar Malaga a ranar Asabar.

Inda me tsaron baya Yerry Mina ya maye gurbinsa a cikin tawagar yan wasan da suka yi tafiyar.

Messi ya sanar da haihuwar dan nasa  shafinsa na Instagram inda ya rubuta sako kamar haka: ” Sannu da zuwa Ciro an gode Allah komai ya tafi dai-dai mahaifiyarsa da shi suna cikin koshin lafiya.Muna cikin farin ciki matuka.”

Wannan ne  da na uku da dan wasan yake da su bayan Thiago mai shekaru 5 da kuma mateo  mai shekaru biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like