Matar marigayi Danbaba Suntai ta daura aure


Hajiya Hauwa Suntai, uwargidan tsohon gwamnan jihar Taraba, Marigayi Danbaba Suntai ta daura aure da Alhaji Sa’ad Malami wanda aka fi sani da Santuraki.

Bikin daurin ya gudana ne ranar Asabar a babban masallacin Abuja.
Hauwa ta koma addinin musulunci kafin ta auri dan kasuwar da ya fito daga jihar Katsina.

Tsohuwar matar gwamnan wacce yar asalin jihar Borno ce kuma tafito ne daga gida na musulmai kafin ta koma addinin Kirista gabanin ta auri Suntai shekarun baya da suka wuce.

Marigayi tsohon maigidan nata yayi hatsarin jirgin sama cikin watan Oktoban shekarar 2012 kafin daga bisani ya mutu a shekarar 2017 a wani asibiti dake birnin Houston can jihar Florida dake Amurka

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like