Betty Anyanwu Akeredolu, matar gwamnan jihar Edo ta kamu da cutar Korona a cewar wasu majiyoyi dake gidan gwamnatin jihar.

Majiyar ta ce tuni matar gwamnan ta killace kanta

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya sanar da cewa ya kamu da cutar.

Majiyar ta kara da cewa,Oluwatoyin Adegbenro matar tsohon kwamishinan lafiya na jihar da ya mutu sanadiyar Korona ita ma ta kamu da cutar.

Inda take samun kulawa a asibitin mijinta dake Akure.

Jaridar The Cable ta wallafa wani rahoto dake cewa yan majalisar dokokin jihar hudu sun kamu da cutar Korona bayan da suka raka gwamnan Abuja ya mika fom dinsa na sake tsayawa takara.