Matar Gwamnan Kebbi, Dakta Zainab Bagudu Ta Yi Bikin Sallah A Gidan Marayu


Mai dakin gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu a jiya Talata ta gudanar da bikin sallah a gidan marayu na Darul Qur’an dake GRA a garin Zuru domin nunawa yaran kauna da jin kai, inda ta ci abinci tare da su.

Dakta Zainab Bagudu ta yi matukar nuna farin cikin ta kan yadda yaran suke samun kulawa, sannan ta baiwa yaran shawarwari irin na iyaye tare da godewa malamansu. Ta kuma kara da cewa koyar da ayyukan hannu yana da muhimmanci a irin wannan gida, wanda hakan zai sa su dogara da kansu bayan ilmin boko da na addini da suka samu.

Daya daga cikin marayun gidan wadda ta yi aure, wato Zainab Bala ta jinjinawa matar gwamnan bisa kaunar da take nuna musu, wanda hakan ya sa ba sa kallon kan su a matsayin marayu.

Shugaban malaman gidan marayun, Malam Umar Abdullahi Rabida da Malama Zainab Idris sun ci gaba da mika godiyar su ga matar Gwamnan bisa kokarin ta na jawo marayun jihar a jiki.

An kuma gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a jihar Kebbi da ma kasa baki daya.

Wasu daga cikin abubuwan da aka gabatarwa marayun sun hada da ķudi, kayan abinci, kayan sawa, kayan kwalliya da sauransu.

Daga cikin wadanda suka yi wa matar gwamnan rakiya, akwai sakataren dindindin na ma’aikatar lafiya, Hajiya Halima Boyi Dikko da Hajiya Zarah Gbashah.

Labari ya fito ne daga hadimar matar gwamnan a fannin yada labarai,
Sabatu Andrew

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like